Matakin first class bai ta'allaka akan karatu kawai ba
Barka da sake saduwa damu a Duniyar Geography. A wannan karon zamu yi hira ne da daya daga cikin daliban da suka yi nassara a gun karatu daga Jami'ar jihar Kaduna (KASU). Don jin yadda muka tattauna, sai ku biyo mu... Masoya Duniyar Geography zasu so sun dan takaitaccen tarihin ka Da farko ina jinjina aikin da kuke yi a duniyar geography. Suna na Salisu Abdulaziz. Ni ne goma, a cikin mu goma sha daya a gidan mu. Duk da iyaye na basu yi karatun boko ba, sun tabbatar da na samu ingantaccen ilimi. Na fara karatu a tarbiyya nursery and primary dake Barnawa, Kaduna daga shekarar 1994 zuwa 2000 inda na karba takardar kammala firamare. Sa'anan naje Jinie college shima a nan Baranawa, Kaduna, nan ma na karba takardar kammala karatun sakandare a shekarar 2006. Salisu Abdulaziz Na rubuta jarabawar shiga jami'a watau JAMB a shekarar 2007. Nayi sa'a na samu shiga jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria (A.B.U) don karanta Architecture. Abubuwa dayawa sun auku ...