Asalin Geography

Barkan ku da war haka da kuma sannun ku da dawowa Duniyar Geography. Zamu fara ne da asali ko tarihin Geography. Don mu san wadanda suka yi rubuce-rubuce da aikace-aikace a tsawon tarihi, don ganin cewa Geography ya kai inda ya kamata. Kamar yadda Turawa ke cewa; "If you don't know where you are coming from, you will not know where you are going". Ma'ana idan baku san inda kuka fito ba, baza kun san inda za ku dosa ba. Haka kuma Hausawa na cewa; "waiwaye adon tafiya". Don haka, a yau tuna baya zamu yi, tare da lissafo wadanda suka taka rawar gani wurin cigaban Geography zuwa iyau. Geography na daga cikin daddadun fanin ilimi. Dayawa cikin Girkawa na ganin Homer ne ya fara rubutaccen Geography wanda aka samu cikin littattafan sa biyu masu taken Iliad da Odyssey wanda littattafan zube ne amma sun na kunshe da Geography masu amfani. Yayi wadan nan ayyukan ne a karni na takwas (8) B.C. A wannan lokaci ba'a fara amfani da kalmar Geography ba don nun...