Latitude da Longitude
Latitude da Longitude, wani hanya ne na musamman don baiwa wurare wani irin adireshi watau coordinates akan doron kasa. Latitude, na nuna inda ko wane wuri yake, Arewaci ko Kudancin Eqautor , wanda awon shi ya kama daga digiri 0° a Equator zuwa digiri 90° a poles. Longitude kuwa, na nuna inda ko wane wuri yake ne, Gabashi ko Yammancin layin prime meridian, awon shi ya kama daga digiri 0° a the prime meridian zuwa digiri 180° a gun da ake ma lakabi da International Date Line . Layin latitude na Equator watau digiri 0° yafi duka layukan latitude fadi kuma yake raba duniya gida biyu; Arewa da Kudu wanda aka fi ma lakabi da Northern and Southern hemispheres. Sauran layukan latitude na rage fadi a yayin da suke matsawa izuwa ga Poles. Layin Equator shine layin latitude mafi muhimmanci akan dukan sauran layukan latitude. Amma layukan longitude duka tsayin su daya ne, wannan yasa kusan dukan suna da muhimmanci. Hakan yasa masu zane suka dinga samun sabani, wanda sai a sh