Posts

Showing posts from May, 2018

Ina ne Najeriya, Su waye Yan Najeriya

Image
A duk lokacin da mutum zai bada bayanin geography na kowanne kasa, to kusan abu daya ne zai yi. Zai fara ne da dubi ne akan wurin, iyakan kasar, girman kasar da kuma manya-manya abubuwan da suka bambanta wannan kasar daga sauran kasashen duniya. Sai kuma dubi akan yanayin kasar wanda ya hada da zahiri (physical), cinikayya kafin dubi na musamman akan mutanen kasar da al’adun su.  Haka zamu bi wajen bada takaittacen karatu game da geography na Najeriya. Zamu duba wurin da Najeriya take zaune, girman kasar da tarihin cigabar kasar da kuma mutanen da ke cikin kasar. Wurin da Najeriya take zaune Najeriya na zaune ne kusan a tsakiyar nahiyyar Afirka. Shi yasa yake daukan lokaci kadan a tafiyar jirgin sama zuwa kowanne waje a Afirka. Daga Legas zuwa Dakar na kasar Senegal sa’o’i kadan ne, kuma kasa da sa’a hudu (4) zuwa Tripoli ko Algiers duk na arewacin Afirka. Tafiyar sa’a uku ne daga Kano zuwa Alkahira; babban birnin kasar Masar. Kuma daidai da lokacin zuwa Addis Ababa na k...