Latitude da Longitude



Latitude da Longitude, wani hanya ne na musamman don baiwa wurare wani irin adireshi watau  coordinates akan doron kasa. Latitude, na nuna inda ko wane wuri yake, Arewaci ko Kudancin Eqautor, wanda awon shi ya kama daga digiri 0° a Equator zuwa digiri 90° a poles. Longitude kuwa, na nuna inda ko wane wuri yake ne, Gabashi ko Yammancin layin prime meridian, awon shi ya kama daga digiri 0° a the prime meridian zuwa digiri 180° a gun da ake ma lakabi da International Date Line.




Layin latitude na Equator watau digiri 0° yafi duka layukan latitude fadi kuma yake raba duniya gida biyu; Arewa da Kudu wanda aka fi ma lakabi da Northern and Southern hemispheres. Sauran layukan  latitude na rage fadi a yayin da suke matsawa izuwa ga Poles. Layin Equator shine layin latitude mafi muhimmanci akan dukan sauran layukan latitude. Amma layukan longitude duka tsayin su daya ne, wannan yasa kusan dukan suna da muhimmanci. Hakan yasa masu zane suka dinga samun sabani, wanda sai a shekarar alif dari takwas da tamanin da hudu (1884) ne aka samu tsayayyen layin longitude wanda yafi muhimmanci.


Wasu daga cikin layukan latitude da ya kamata ku sani:

Ø  North pole wanda yake kan digiri tasa’in (90) Arewacin Equator
Ø  Arctic circle wanda yake kan digiri sittin da shida da rabi (661/2 ) Arewacin Equator
Ø  Tropic of Cancer wanda yake kan digiri ashirin da uku da rabi (231/2 ) Arewacin Equator
Ø  Tropic of Capricorn wanda yake kan digiri ashirin da uku da rabi (231/2 ) Kudancin Equator
Ø  Antartic circle wanda yake kan digiri sittin da shida da rabi (661/2 ) Kudancin Equator
Ø  South pole wanda yake kan digiri tasa’in (90) Arewacin Equator



Layin 0° na longitude ya bi ta Landan a inda ake kira da Greenwich Observatory har zuwa Accra a kasar GhanaKo wane layin digiri na latitude da longitude ya rabu izuwa mintuna sittin (60), kuma ko wane minti ya rabu izuwa dakika sittin (60). Hakan yasa ko wane wuri a fadin duniya na ayyananen lambobin coordinates wanda yake zama tamkar adireshin wannan wurin. Ana amfani da layukan latitude wurin lissafin nisa tsakanin wurare biyu a doron kasa. Layukan longitude kuwa ana amfani da su wurin lissafin bambanci lokaci daga wuri zuwa wuri.

Ana iya daukan latitude da longitude da na’ura ta musamman wanda ake kira GPS. A yau wayoyin hannu suna zuwa dauke da GPS wanda zaku iya mafani da don daukan coordinates din gun da kuke.
 



Comments

  1. Thank you for this. Beautifully written. 🙌

    ReplyDelete
    Replies
    1. Mun gode. Da fatan zaka sake ziyarar shafin

      Delete
  2. Ina Mika godiya ta musamman biga wannan cikekken baya da ka yi,

    ReplyDelete
  3. daeliWnipa_Billings Tom Larson Here
    viespirzivi

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

Asalin Geography

Tsarin Duniya (Structure of the Earth) kashi na daya