Maraba da Duniyar Geography

Geography wani bangare ne na kimiyya da ke nazarin siffofin duniya ( sararin samaniya (atmosphere), kasa (lithosphere), ruwa (hydrosphere), kankara (cryosphere), rai (biosphere) da sauran su, da kuma ayyukan ɗan adam da yadda take shafar shi, ciki har da rarrabuwan jama'a da albarkatu da ayyukan siyasa da tattalin arziki. 


An samo wannan hoto daga thinklink.com


Geography fanin karatu ne da aka dade ana masa mummunar fassara ko in ce fahimta. Wanda akwai fittcen labarin nan da wani dalibi da bai gane karatun Geography yake tambayan mai tallan maganin gargajiya, ko yana da maganin Geography? amsan da ya fito daga bakin mai tallan maganin nan shine: "Joga-Joga Mugun ciwo, shi ya kashe kaka na". Duk wani da zaka samu yana samun cikas a fahimtar Geography, da zaran ka tambaye me yasa bai ganewa, amsan dai zai fara fitowa daga bakin sa shine: " Joga- Joga Mugun ciwo". 

Duniyar Geography ta fito ne don dinke wannan gibi. Duniyar Geography zata sauwake Geography ta yadda Hausawa ko masu karatu da harshen Hausa zasu samu sauki gun fahimtar Geography tare da fayyace duk sarkakiya da ke cikin fahimtar ta. Muna Maraba da tambayoyi da shawarwarin ku. Mun gode.

Comments

  1. Replies
    1. Nagode Yenok Andrew. Da fatan zaka sake ziyarar shafin.

      Delete
  2. Allah Ya sa a daure dan uwa, aiki ne mai kyau da muhimmanci sai dai yana bukatar jajircewa da hakuri, domin irin wadannan ilimomi sun yi karanci a cikin al'ummar Hausawa. Allah Ya sanya albarka

    ReplyDelete
  3. Gaskiya wannan zai ƙara ma masu karatu fahimtan darasin. Allah ya taimaka.

    ReplyDelete
    Replies
    1. Nagode Harith Yusuf. Da fatan zaka sake ziyarar shafin.

      Delete
  4. Wannan shafi na yanar gizo gizo mai dauke da bayanan ilmin sanin ƙasashe, teku, yawan jama'a da dai sauransu. Ba shaka zai kara iliman tar jama'a a hausan ce. muna godiya kuma Allah ya taimaka.

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

Asalin Geography

Latitude da Longitude

Tsarin Duniya (Structure of the Earth) kashi na daya