Matakin first class bai ta'allaka akan karatu kawai ba
Barka da sake saduwa damu a Duniyar Geography. A wannan karon zamu yi hira ne da daya daga cikin daliban da suka yi nassara a gun karatu daga Jami'ar jihar Kaduna (KASU). Don jin yadda muka tattauna, sai ku biyo mu...
Masoya Duniyar Geography zasu so sun dan takaitaccen tarihin ka
Masoya Duniyar Geography zasu so sun dan takaitaccen tarihin ka
Da farko ina jinjina aikin da kuke yi a duniyar geography. Suna na Salisu Abdulaziz. Ni ne goma, a cikin mu goma sha daya a gidan mu. Duk da iyaye na basu yi karatun boko ba, sun tabbatar da na samu ingantaccen ilimi. Na fara karatu a tarbiyya nursery and primary dake Barnawa, Kaduna daga shekarar 1994 zuwa 2000 inda na karba takardar kammala firamare. Sa'anan naje Jinie college shima a nan Baranawa, Kaduna, nan ma na karba takardar kammala karatun sakandare a shekarar 2006.
![]() |
Salisu Abdulaziz |
Na rubuta jarabawar shiga jami'a watau JAMB a shekarar 2007. Nayi sa'a na samu shiga jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria (A.B.U) don karanta Architecture. Abubuwa dayawa sun auku da yayi sanadiyar rashin kammala wannan karatun. Bayan barin A.B.U na sake rubuta wani JAMB. Na kara sa'a, na shiga jami'ar jihar Kaduna (KASU) don karanta geography.
Ko zamu iya sanin sirrin da ka rike har ka cin ma wannan nassara?
Babu wani siddabaru ko sirri game da matakin first class da na fita da shi. Naci, dagiya da tsuran aiki tare da addu'o'i su na rike yayin karatu na. Bayan haka na yi sa'an wasu zakakurai, wadan da na koyi abubuwa dayawa a gun su. Wadan nan sune Nazir M. Chobal, Muhammad Lawal Abubakar da Mustapha Aliyu Terry. Sune zan iya cewa sun tabbatar da ina wannan matakin. Nagode ma Allah kuma nagode da kokarin da suka yi min.
Wane fanni ne ka fi so a cikin Geography?
Ban karanci geography ba a makarantan sakandare, shi yasa da farko bani da shauki game da karatun. Kawai ina karatu ne don na wuce wurin kaman yadda kowa yake cewa da yadda ake bukata daga gare mu. Daga baya karatun geography ya shiga rai na sosai musamman climatology.
A duk wani iri abu da mutum zai yi, ya kan gaji ko ya samu sanyi gwiwa, shin mene ne ya baka kwarin gwiwa har ka samu wannan nassarar?
Abun da yake bani kwarin gwiwa don dagewa akan karatu, ba komai bane face mahaifiya ta. Ta rasu dan satuttuka kafin na shiga KASU. Ta so ni da karatu matuka, don haka shi yasa na dage akan karatun har na kai wannan matakin. Abokai na ma sun bani karin kwarin gwiwa a fannoni daban-daban a lokacin da muke jami'a.
![]() |
Takardar Shaidar kammala karatun Digiri a fannin Geography a matakin "first class" |
Idan zaka koma baya, watau ka sake daga farko. Me da me zaka yi, kuma wasu abubuwa zaka guje ma?
Bana so na koma baya ko kadan, don an sha gwagwarmaya daban-daban. Toh sai dai idan zan cigaba da da karatu zan fuskance shi ne da kyau fiye da yadda nayi a baya.
Mutane da dama idan ake wane ya rike takardar digiri da matakin "first class", ana mai kallon cewa littafi kadai ya sani, duka lokacin sa wurin karatu yake karewa. Shin ya hakan yake?
Abokai na zasu iya shaida ni ba irin mutanen ne ba da ake kira nerds ba ko yadda gayu ke cewa masu cin littafi. Ina karatu ne lokacin da ake bukata na da nayi. Bayan nan kuma na kan yi karatu duk lokacin da naga ya dace nayi. Ina wasu shagulgula kamar kowa. Zan iya cewa nafi dayawa shagala a cikin yan ajin mu. Fita da matakin first class bai ta'allaka akan karatu kawai bane. Sanin abin da ya dace, yin abin da ya dace a lokacin da ya dace shi ne gaba da komai.
![]() |
Salisu Abdulaziz a iska yayin murnar kammala karatu |
Muna fata wannan dan takaitaccen hirar zai farkar da matasa da dalibai akan dagewa wajen samun sakamako mai kyau a jami'a, kuma zasu yi koyi da abu daya ko biyu daga tattaunawar mu da Salisu Abdulaziz. Wadan da kuma suke kokari sai su kara hakuri da dagewa har lokacin kammala karatu.
Godiya ta musamman ga Salisu Abdulaziz da ya bamu lokaci har muka samu muka yi wannan hirar. Ba za mu manta da Abdulaziz Hassan ba; wanda ya zana Dagin Duniyar Geography. Mun gode. Da haka ne muka kawo karshen wannan karon. Kar ku manta ku rubuta tambayoyi ko shawarwari a akwatin sharhi watau "comment box". Zaku iya bin mu a shafin mu na Facebook. Haka zaku iya samun sabon darasi da dumi-dumin su idan kuka danna "subscribe" a sama.
Comments
Post a Comment