Ina ne Najeriya, Su waye Yan Najeriya
A duk lokacin da mutum zai bada bayanin geography na
kowanne kasa, to kusan abu daya ne zai yi. Zai fara ne da dubi ne akan wurin,
iyakan kasar, girman kasar da kuma manya-manya abubuwan da suka bambanta wannan
kasar daga sauran kasashen duniya. Sai kuma dubi akan yanayin kasar wanda ya
hada da zahiri (physical), cinikayya kafin dubi na musamman akan mutanen kasar da al’adun
su. Haka zamu bi wajen bada takaittacen karatu game da
geography na Najeriya. Zamu duba wurin da Najeriya take zaune, girman kasar da
tarihin cigabar kasar da kuma mutanen da ke cikin kasar.
Wurin da Najeriya take zaune
Najeriya na zaune ne kusan a tsakiyar nahiyyar
Afirka. Shi yasa yake daukan lokaci kadan a tafiyar jirgin sama zuwa kowanne
waje a Afirka. Daga Legas zuwa Dakar na kasar Senegal sa’o’i kadan ne, kuma
kasa da sa’a hudu (4) zuwa Tripoli ko Algiers duk na arewacin Afirka. Tafiyar
sa’a uku ne daga Kano zuwa Alkahira; babban birnin kasar Masar. Kuma daidai da
lokacin zuwa Addis Ababa na kasar Etofiya.
Kasar tana zaune ne akan layukan longitude digiri 3
zuwa 15 gabas da Greenwich. Najeriya na zagaye da kasashe masu Magana da
harshen Faransa na Afirka ta yamma, ban da ta kudu; inda kasar ke da iyaka da
tekun Atlantic. Najeriya na da iyaka da kasar Benin ta yamma, kasar Nijar ma’abociya
Hamada ta arewa da kuma kasar Kamaru ta gabas.
Najeriya na zaune har iyau akan layukan latitude digiri
4 zuwa 14 arewacin equator. Haka yasa Najeriya ke karkashin iskoki biyu na “westerlies”
da ‘easterlies” wanda suke yawo lokaci-lokaci a kasar, wanda yake kawo sauyin
yanayi a kasar. Wannan yankin latitude da Najeriya take kai na mata amfani wajen
samun ruwan sama, sanyi, zafi, da kurar hunturu. Wurin da kasar take wuri ne mai amfani saboda ba'a kulle take ba watau "landlocked", saboda tana da teku wanda ke da matukar amfani wuri safara, samun ruwa don aikace-aikace daban daban, hakan ma'adinai musamman man fetur da sauran su.
Girman kasa
Mafi nisan tafiya daga gabas zuwa yamma a Najeriya
kimanin kilomita dubu daya da dari hudu ne (1400), sa’anan daga arewa zuwa kudu
kimanin kilomita dubu daya da dari daya ne (1100). Najeriya na da fadin kasa da
ya kai kilomita sikwaya 923700. Najeriya tayi girman kasar Ghana sau hudu, sa’anan
tayi girman kasar Saliyo sau goma sha uku (13). Najeriya na dauke da kasha daya
bias bakwai na fadin kasan Afirka ta yamma.
Yadda aka samu
Najeriya
Najeriya a daba kasa daya bace kamar yadda muka
santa a yau. Yankin a da tana kunshe da garuruwa da dauloli manya da kanana. Daga
cikin wadannan dauloli, Daular Usmaniyya tafi kowanne girma da shahara. Daular
ta shafe gaba dayan arewacin Najeriya a karni na sha tara. A kudu kuwa akwai
Oyo da Benin. A kudu maso gabas akwai Inyamurai da Ibibio a kananan kauyuka. An
samu Najeriya ne a shekarar 1914 bayan hade kudanci da arewacin Najeriya wanda
turawan mulkin mallaka suka yi.
Yan Najeriya
Mutanen da kuke gani a hoton da ke kasa kadan kenan
daga cikin mutane kimanin miliyan dari da tasa’in (190) dake zaune a Najeriya.
Yawan mutanen Najeriya miliyan talatin da daya ne a shekarar 1953, miliyan
hamsin da biyar a shekarar 1963. A kidayan shekarar dubu biya da biyu (2002)
yawan yan Najeriya ya kai miliyan dari da arba'in.
Ba shakka Najeriya itace kasar da tafi kowanne yawan
mutane a Afirka.
Wasu daga cikin
yan Najeriya
Fulani:
suna zaune tare da Hausawa ne amma sun fi yawa a jihar Filato da Adamawa. Fulanin
asali dogaye ne, marasa jiki, suna da siraran hanci da gashi baki mai tsawo. Fatan
jikin sun a da haske.
Kanuri: suna zaune a arewacin Najeriya a jihar Barno,
Bauchi da Adamawa
Yarbawa: ana samun su ne a jihar Oyo, Ogun, Ondo da Legas.
Akwai Yarbawa a jihar Kwara da kasar Benin.
Inyamurai: suna zaune a jihar Anambra, Imo, Rivers da Delta
Ibibio: suna zaune a Uyo, Annang, Eket da Opobo duk a
jihar Cross Rivers. Suna kama da Inyamurai sai dai suna da bambancin al’adu.
Sauran mutanen Najeriya; sun hada da Nufawa, Jukunawa, Gwari, Katafawa, Ibira, Igala, Gwandara, Kaje, Tibi, Ijaw, Kabba, Ikulu, Efik da sauran su.
Sauran mutanen Najeriya; sun hada da Nufawa, Jukunawa, Gwari, Katafawa, Ibira, Igala, Gwandara, Kaje, Tibi, Ijaw, Kabba, Ikulu, Efik da sauran su.
Anan
muka kawo karshen karatun mu na wannan karo, don Karin bayani a tuntube mu ta
shafin mu na facebook a @duniyargeography, haka kuma zaku iya bin tashan mu na youtube idan kuka sa Duniyar Geography ko ku danna nan. Sai mun
sake saduwa. Ma’assalam!
Mujin dadin ilmantarda mu
ReplyDelete