RANAR MUHALLI 2018

Biyar ga watan Yuni na kowace shekara rana ce ta musamman. Rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware musamman don muhalli. Ana bukukuwa daban-daban ne a wannan rana. Ya hada taruka don karawa juna sani, aikin gayya don tsaftace muhalli, tattaki da sauran su. Taken bikin na wannan shekarar shi ne “Beat Plastic Pollution” watau yadda za’a kawo karshen gurbacewar muhalli a sanadiyar robobi. Robobi sun zama kaya ko ababen amfanin dan Adam na yau da kullum saboda daidaikun abubuwa ne ba’a yi su da roba ba, ko ba na roban su. A kasar mu robobi da aka fi amfani dasu sun hada da; ledar ruwa, ledar sanya kaya, butoci, gorar ruwan sha, bangarorin mashina da motoci da dai sauran su. Robobi ana masu lakabi da “non-biodegradable” wato basu iya rubewa, su bi kasa a cikin kankanin lokaci. Masana sun nuna shekara dari hudu da hamsin zuwa shekara dubu daya ya ke daukan robobi kafin su rube. Bayan haka suna kunshe da wasu sinadirai da ake da okzidants (oxidan...