RANAR MUHALLI 2018
Biyar
ga watan Yuni na kowace shekara rana ce
ta musamman. Rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware musamman don
muhalli. Ana bukukuwa daban-daban ne a wannan rana. Ya hada taruka don karawa
juna sani, aikin gayya don tsaftace muhalli, tattaki da sauran su.
Taken
bikin na wannan shekarar shi ne “Beat Plastic Pollution” watau yadda za’a kawo
karshen gurbacewar muhalli a sanadiyar robobi.
Robobi
sun zama kaya ko ababen amfanin dan Adam na yau da kullum saboda daidaikun
abubuwa ne ba’a yi su da roba ba, ko ba na roban su. A kasar mu robobi da aka
fi amfani dasu sun hada da; ledar ruwa, ledar sanya kaya, butoci, gorar ruwan
sha, bangarorin mashina da motoci da dai sauran su. Robobi ana masu lakabi da “non-biodegradable”
wato basu iya rubewa, su bi kasa a cikin kankanin lokaci. Masana sun nuna
shekara dari hudu da hamsin zuwa shekara dubu daya ya ke daukan robobi kafin su rube. Bayan haka suna kunshe
da wasu sinadirai da ake da okzidants (oxidants) da suke da illa ga dabbobi da
dan Adam.
Dabbobi
musamman na ruwa da kifaye sun fi samun barazanar robobi. Saboda robobi na
karewa ne akan tituna zuwa magudanan ruwa har zuwa tekuna. Sa’anan robobi na
toshe ma kifayen iska akan tekuna, tare da sake sinadarin okzidant wanda su
kadai mai sun isa kasha kifayen.
![]() |
Hoto : apeuk.org |
Dan Adam kuma ya na rasa ko samun karancin
kifaye tare da cin guban da ke cikin wadan nan kifayen. Sauran illolin robobi
sun hada da:
- Karanci kudin shiga ga masu sana’ar su
- Samun cutar cancer cikin sauki
- Munana muhalli
- Toshe magudanan ruwa
- Ambaliya da sauran su.
Duniyar
Geography ta samu halartar daya daga cikin taruka da aka yi wannan ranar a
jihar Kaduna.
Bridge that Gap da Citizen Climate Lobby da goyon bayan kungiyoyin muhalli, chanjin yanayi da
makamantan su ne suka shirya wannan taro wanda ya wakana a Kaduna ICT Hub.
Taron
ya samu halartar malamai da masana a fannin muhalli, kamfanonin robobi, manoma, dalibai, masu fafutuka akan muhalli, yan jarida da sauran su.
Cikin
malaman da suka yi bayani sun hada da Dr. Bashir Sodipo daga sashen Kimiyyar Lissafi (Physics) na jami’ar jihar Kaduna. Yayi bayani ne akan yadda za’a amfana daga dubannin
bololin robobi da ke waste a ko ina. Ya fara da nuna cewa matsalar gurbatan
muhalli sanadiyar robobi matsala ce da kasashen duniya ce fama da shi. Ya ce
kasar Turkiyya ce kadai ta iya sarrafa rabin bololin robobin ta. Kasar Indiya
kuwa suna ta nazari akan samo sabbobi amfanin robobi, inda ya nuna sun yi
nasara wajen yin tituna da robobi a maimaikon kwalta.

Ya
ce kuma akwai sabon hanya da za’a iya sa robobi su dinga rubewa. Ya ce hakan na
yiwuwa ne ta abin da ake kira da “nanotechnology”. Za’a samu wasu sinadirai
daga itatuwa a sanya a cikin robobi a yayin da ake hada su ko sarrafa su. Idan
aka yi haka robobi za su zama “biodegradable”. Amma sai dai zasu kawo rashin
daidaito a cikin muhalli don zasu kara yawo sinadirai a kasa, iska da ruwa
wanda hakan zai jawo matsaloli daban-daban.
Dr.
Sodipo ya ce idan aka yi kayan fashewa kamar gilas da tangaran da makamantan su
tare da robobi, za su kasance da arha kuma zasu yi karko sosai fiye da yadda
ake tsammani. Sai dai ya nuna wannan sabon salo zai kirkiro sabbobin matsaloli
ne da zasu bukaci nazari na musamman akai. Saboda za’a samu kudi kuma aji dadi
amma sai bayan wasu shekaru ne za’a ga illolin wannan sabon salon.
Sauran masu Jawabi sun hada Tabi Joda, Gloria Bulus, Hamzat Gambo da sauran su.
Don rage wasu daga cikin illolin robobi, zai yi kyau ku dauki wadan nan shawarwari;
- Kuyi amfani da leda fiye da sau daya
- Ku rage sayan kaya da aka yi su da roba
- Ku dai cin abinci cikin roba ko leda
- Ku daina zubar da robobi akan tituna, magudanan ruwa ko rafuka
- Idan zaku yi amfani da leda ku tabbata tana da tambari "recycle"
Don
ganin yadda bukin muhalli na wannan shekara ta wakana, ku bi #WorldEnvironmentDay
#WED #WED2018 #WEDKaduna #BeatPlasticPollution a shafukan zumunta na facebook
da twitter inda zaku sami rubuce-rubce, hotuna da bidiyoyi da zaku iya saukewa
akan na’urar ku. Kar ku manta ku bi Duniyar Geography a facebook
@duniyargeography.
Comments
Post a Comment