Asalin Geography


Barkan ku da war haka da kuma sannun ku da dawowa Duniyar Geography. Zamu fara ne da asali ko tarihin Geography. Don mu san wadanda suka yi rubuce-rubuce da aikace-aikace a tsawon tarihi, don ganin cewa Geography ya kai inda ya kamata. Kamar yadda Turawa ke cewa; "If you don't know where you are coming from, you will not know where you are going". Ma'ana idan baku san inda kuka fito ba, baza kun san inda za ku dosa ba. Haka kuma Hausawa na cewa; "waiwaye adon tafiya". Don haka, a yau tuna baya zamu yi, tare da lissafo wadanda suka taka rawar gani wurin cigaban Geography zuwa iyau.

Geography na daga cikin daddadun fanin ilimi. Dayawa cikin Girkawa na ganin Homer ne ya fara rubutaccen Geography wanda aka samu cikin littattafan sa biyu masu taken Iliad da Odyssey  wanda littattafan zube ne amma sun na kunshe da Geography masu amfani. Yayi wadan nan ayyukan ne a karni na takwas (8) B.C. A wannan lokaci ba'a fara amfani da kalmar Geography ba don nuni da wannan fanin ilimin ba.
                                    
Geography dai ya samo asali ne daga kalmar Girkanci (γεωγραφία) watau "geographia", fassarar ma'anar zai zama "bayyana ko rubutu game da Duniya". Mutumin farko da yayi amfani da kalmar "geography" shine Eratosthenes (276-194 BC).
Erastosthenes



Eratosthenes Bagirke ne, masanin lissafi, mashahurin geographer, mawaki, masani a ilimin wata da taurariMalami ne kafin ya zama babban masanin littattafai (Chief Librarian) a dakin karatu na Al’iskandaria na kasar Masar (Library of Alexandria)Ya shahara ne domin shine mutum na farko da yayi lissafin kewayen duniya watau (circumference of the earth), kuma lissafinya zamo daidai. Ya kuma kididdige nisa daga Duniya zuwa rana, da kuma abin da ake kira da “leap year”Shi ya fara zana taswirar duniya, tare da sa layukan “parallels na latitude” da meridians na longitude” daidai da ilimin dake samuwa a zamaninsa. Wadan nan, watau (Longitude da Latitude) karatu ne masu zaman kan su da zamu yisu a nan gaba idan muna da yawanci raiA cikin littafinsa mai mujalladi uku mai take; "Geographika", Erastosthenes yayi bayyani da kuma zana dukkanin sanannun wurare a duniyan lokacin, har ma da raba Duniya zuwa yanki biyar mabambanta yanayi: yankunan daskarewa guda biyu a kusa da "poles", yankuna biyu da ke cikin yankin "temperate", da kuma yanki daya da kunshe da "equator"  da "tropics" da sauran abubuwa da baza su lissafu a nan ba.

Domin karin bayanin gameda tarihi da gudunmawa da Erastosthenes ya bada a Geography, zaku so ku duba wadan nan shafukan;  Erastosthenes Experiment, Encyclopaedia Britannica da Wikipedia.


Akwai masana da dama da suka taka rawar gani a Geography wanda zamu lissafo sunayen su ne kawai, nan gaba zamu dauke daya bayan daya mu ji duk irin gudunmawan da suka bada. Wadan nan sun hada da Ptolemy, Alexander Von HumboldtCarl Ritter, Ibn Khaldun, StraboWilliam Morris DavisWaldo ToblerXu XiakeYaqut Al Hamawi, Liu An da sauran su.

Kadan kenan daga cikin tarihin Geography inda muka tabo gudunmawa da "Baban Geography" watau Erastosthenes yayi wanda ya kawo Geography martabar da yake. Mun gode da daukan lokaci na musamman dun ziyarar wannan shafi da karanta wannan dan takaitaccen rubutu. Da fatan yayi muku amfani. Ina sauraron shawarwari da tambayoyin ku a akwatin sharhi (comment box). Sai wani jikon kuma.







Comments

  1. wannan ci gaba ne mai matukar amfani,Allah yasa ya daure.

    ReplyDelete
  2. Sannu da kokari Allah sa yafi haka

    ReplyDelete
  3. Yanzu dai Geography ba ciwo bane kuma, don't mun sami cigaba.

    ReplyDelete
    Replies
    1. hahah, wannan gaskiya ne Malan Danlami Dogonyaro. Nagode

      Delete
  4. Yanzu dai Geography ba ciwo bane kuma, don't mun sami cigaba.

    ReplyDelete


  5. Gaskiya wannan lamari na yi farin ciki da shi so sai. Lokaci ya iso da ya kamata murinka koyar da kanmu ilimi cikin luggar hausa... Allah ya ka ra basira da ilimi.

    ReplyDelete
  6. Wannan haka yake Mal Abdul, nagode kwarai da gaske. Allah ya saka da alheri

    ReplyDelete
  7. Allah yakara basira

    ReplyDelete
  8. Allah ya kara mana ilimi mai albarka Amen

    ReplyDelete
  9. Allahamdulillah gaskiya yayi

    ReplyDelete
  10. Gaskiya ne allah kakara mana ilmi

    ReplyDelete
  11. Respect and I have a keen offer: How Much Remodel House updating exterior of home

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

Latitude da Longitude

Tsarin Duniya (Structure of the Earth) kashi na daya