Asalin Geography
Barkan
ku da war haka da kuma sannun ku da dawowa Duniyar Geography. Zamu fara ne da
asali ko tarihin Geography. Don mu san wadanda suka yi rubuce-rubuce da
aikace-aikace a tsawon tarihi, don ganin cewa Geography ya kai inda ya kamata. Kamar
yadda Turawa ke cewa; "If you don't know where you are coming from, you
will not know where you are going". Ma'ana idan baku san inda kuka fito
ba, baza kun san inda za ku dosa ba. Haka kuma Hausawa na cewa; "waiwaye
adon tafiya". Don haka, a yau tuna baya zamu yi, tare da lissafo wadanda
suka taka rawar gani wurin cigaban Geography zuwa iyau.
Geography na daga cikin daddadun fanin ilimi. Dayawa cikin Girkawa na ganin Homer ne ya fara rubutaccen Geography wanda aka samu cikin littattafan sa biyu masu taken Iliad da Odyssey wanda littattafan zube ne amma sun na kunshe da Geography masu amfani. Yayi wadan nan ayyukan ne a karni na takwas (8) B.C. A wannan lokaci ba'a fara amfani da kalmar Geography ba don nuni da wannan fanin ilimin ba.
Geography na daga cikin daddadun fanin ilimi. Dayawa cikin Girkawa na ganin Homer ne ya fara rubutaccen Geography wanda aka samu cikin littattafan sa biyu masu taken Iliad da Odyssey wanda littattafan zube ne amma sun na kunshe da Geography masu amfani. Yayi wadan nan ayyukan ne a karni na takwas (8) B.C. A wannan lokaci ba'a fara amfani da kalmar Geography ba don nuni da wannan fanin ilimin ba.
Geography dai ya samo asali ne daga kalmar Girkanci (γεωγραφία) watau "geographia", fassarar ma'anar zai zama
"bayyana ko rubutu game da Duniya". Mutumin farko da yayi amfani da
kalmar "geography" shine Eratosthenes (276-194
BC).
|
Eratosthenes Bagirke ne, masanin lissafi, mashahurin geographer,
mawaki, masani a ilimin wata
da taurari. Malami ne kafin ya zama babban
masanin littattafai (Chief
Librarian) a dakin karatu na Al’iskandaria na kasar Masar (Library of Alexandria). Ya shahara ne domin shine mutum na farko da yayi lissafin kewayen duniya watau (circumference of the earth), kuma
lissafinya zamo daidai.
Ya kuma kididdige
nisa daga Duniya zuwa rana, da kuma abin da ake kira da “leap year”. Shi ya fara zana taswirar
duniya, tare da sa layukan
“parallels na latitude” da meridians na longitude” daidai da ilimin dake samuwa a
zamaninsa. Wadan nan, watau
(Longitude da Latitude) karatu ne masu zaman kan su da zamu yisu
a nan gaba idan muna da yawanci rai. A
cikin littafinsa mai mujalladi uku
mai take; "Geographika", Erastosthenes yayi bayyani da kuma zana dukkanin sanannun wurare a duniyan lokacin, har ma da raba
Duniya zuwa yanki biyar
mabambanta yanayi:
yankunan daskarewa guda biyu
a kusa da "poles",
yankuna biyu da ke cikin yankin "temperate",
da kuma yanki daya da kunshe da "equator" da "tropics" da sauran abubuwa da baza su lissafu a nan ba.
Domin karin bayanin
gameda tarihi da gudunmawa da Erastosthenes ya bada a Geography, zaku so ku
duba wadan nan shafukan; Erastosthenes
Experiment, Encyclopaedia Britannica da Wikipedia.
Akwai masana da dama
da suka taka rawar gani a Geography wanda zamu lissafo sunayen su ne kawai, nan
gaba zamu dauke daya bayan daya mu ji duk irin gudunmawan da suka bada. Wadan
nan sun hada da Ptolemy, Alexander Von Humboldt, Carl Ritter, Ibn Khaldun, Strabo, William Morris Davis, Waldo Tobler, Xu Xiake, Yaqut Al Hamawi, Liu An da sauran su.
Kadan kenan daga cikin
tarihin Geography inda muka tabo gudunmawa da "Baban Geography" watau
Erastosthenes yayi wanda ya kawo Geography martabar da yake. Mun gode da daukan
lokaci na musamman dun ziyarar wannan shafi da karanta wannan dan takaitaccen
rubutu. Da fatan yayi muku amfani. Ina sauraron shawarwari da tambayoyin ku a
akwatin sharhi (comment box). Sai wani jikon kuma.
wannan ci gaba ne mai matukar amfani,Allah yasa ya daure.
ReplyDeleteAmin. Nagode Kwarai Ace Khalifa.
DeleteSannu da kokari Allah sa yafi haka
ReplyDeleteAmin. Nagode Abdul Muh'd Yaro.
DeleteAllah yasa albarka
ReplyDeleteAmin. Allah ya saka da alheri. Nagode
DeleteYanzu dai Geography ba ciwo bane kuma, don't mun sami cigaba.
ReplyDeletehahah, wannan gaskiya ne Malan Danlami Dogonyaro. Nagode
DeleteYanzu dai Geography ba ciwo bane kuma, don't mun sami cigaba.
ReplyDelete
ReplyDeleteGaskiya wannan lamari na yi farin ciki da shi so sai. Lokaci ya iso da ya kamata murinka koyar da kanmu ilimi cikin luggar hausa... Allah ya ka ra basira da ilimi.
Wannan haka yake Mal Abdul, nagode kwarai da gaske. Allah ya saka da alheri
ReplyDeleteAllah yakara basira
ReplyDeleteAllah ya kara mana ilimi mai albarka Amen
ReplyDeleteAllahamdulillah gaskiya yayi
ReplyDeleteGaskiya ne allah kakara mana ilmi
ReplyDeleteRespect and I have a keen offer: How Much Remodel House updating exterior of home
ReplyDelete